Masallacin Ketchaoua | |
---|---|
Casbah na Algiers | |
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Aljeriya |
Province of Algeria (en) | Algiers Province (en) |
Mazaunin mutane | Aljir |
Coordinates | 36°47′06″N 3°03′38″E / 36.785°N 3.0606°E |
History and use | |
Opening | 1612 |
Addini | Musulunci |
Karatun Gine-gine | |
Style (en) | Islamic architecture (en) |
Heritage | |
Parts | Hasumiya: 2 |
|
Masallacin Ketchaoua (Larabci: جامع كتشاوة, Djamaa Ketchaoua) masallaci ne a Algiers, babban birnin Algeria. An gina ta a lokacin daular Usmaniyya a cikin karni na 17 kuma tana nan a gindin Casbah, wanda yake wurin tarihi ne na UNESCO. Masallacin na tsaye ne a farkon hawa na Casbah mai yawan matattakalai kuma ya kasance cikin tsari da alama alamomi ne na kafin mulkin mallaka rna Algiers.[1][2][3] Masallacin an san shi saboda haɗakarwa ta musamman na gine-ginen Morish da Byzantine.[4]
Asalin an gina masallacin ne a shekarar 1612. Daga baya kuma, a shekarar 1845, aka canza shi a lokacin mulkin Faransa, zuwa Cathedral na St Philippe, wanda ya ci gaba har zuwa 1962. An rushe tsohon masallacin tsakanin 1845 da 1860 kuma an gina sabon coci. An canza shi zuwa masallaci a 1962. Duk da wadannan sauye-sauye a kan addinai mabambantan addinai a cikin karnoni hudun da suka gabata, masallacin ya ci gaba da rike matsayinsa na asali kuma yana daya daga cikin manyan abubuwan jan hankali na Algiers.[4][5]
© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search